
Jirgin yaki na sojojin Najariya ya kashe ‘yan Bìndìgà 23 a garin Tsafe dake jihar Zamfara.
An kashe ‘yan Bindigar ne a wannan karshen makon da muke ciki.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan Bindiga da yawa dake karkashin dan Bindiga Ado Aleiro sun bar tsafe inda suka tafi dan kai hari da satar shanu a wasu kauyuka.
Rahoton yace ‘yan Bindigar sun yi nasarar kwace shanun duk da mutanen garin sun dan musu Turjiya, a yayin da suke kokarin guduwa da shanun ne sojojin Najariya suka gansu suka bude musu wuta.
Shaidu sun bayyana cewa an kashe ‘yan Bindigar da yawa inda wasu suka ce sun ga gawarwakin 23 daga cikinsu.
Daga baya dai sojojin sun kwace shanun da ‘yan Bindigar suka kwato.