Tuesday, May 19
Shadow

Dalilin da yasa na kifar da gwamnatin Buhari duk da yake cewa nine shugaban ma’aikatansa>>IBB ya magantu

Tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida,IBB ya bayyana dalilin da yasa ya kifar da Gwamnatin tsohon shugaban kasa, Janar Muhammadu Buhari.

Ya bayyana hakane a littafinsa da ya wallafa wanda yayi bayani kan yanda ya gudanar da aikinsa.

IBB wanda shine shugaban ma’aikatan Gwamnatin Buhari a wancan lokacin yace bai gamsu da yanda Buhari ke gudanar da mulki ba shiyasa ya masa juyin mulki.

IBB yace tare suke mulki amma sam yaga tsare-tsaren Buhari basa kawo ci gaba a kasar shiyasa ya kifar dashi a shekarar 1985.

Karanta Wannan  Wannan Jari Ne Na Naira Dubu 500 Wanda Na Yi Alkawarin Zan Baiwa Duk Wanda Zai Aure Ni, Kawai Abinda Za Ka Yi Shine Ka Ajiye Min Hotonka, Zan Duba Na Gani Idan Ka Yi Min Zan Yi Ma Magana, Cewar Wannan Budurwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *