
Wani magidanci dake tsakanin shekaru 30 ya fashe da kuka bayan da matarsa ta haifi ‘yan 6.
Bidiyon lamarin ya watsu a kafafen sada zumunta inda akai ta zazzafar muhawara akai.
Mutumin ya tsaya kan matarsa inda ya rika fadin lallai kina da karfin hali da kika iya haifar ‘yan shida.
Rahotanni sun ce mutumin na tunanin kudin kula da yaran ne shiyasa shi kuka.
!An dai ga Ma’aikaciyar jinya tana bashi baki kan lamarin.