‘Yansanda a Ota dake jihar Ogun sun kama wani mutum me suna Olubunmi Johnson dan kimanin shekaru 55 saboda kunnawa matarsa wuta.
Lamarin ya farune da misalin karfe 8:30 pm na ranar Juma’ar data gabata a gidansu dake kan titin Fagbuyi na yankin Ilogbo.
Wanda ake zargin ya jike matarsa da man fetur sannan ya kunna mata wuta.
Kakakin ‘yansandan jihar, Omolola Odutola ta bayyana cewa, dangin matar ne suka sanar dasu abinda ke faruwa.
Tace an garzaya da matar zuwa Asibiti inda shi kuma mijin aka kamashi inda ake bincikensa kan yunkurin yin kisa.