Monday, December 9
Shadow

Peter Obi ya baiwa daliban Najeriya shawarar su tafi kasar waje dan neman saukin rayuwa

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party a zaben shekarar 2023 da ta gabata, Peter Obi ya baiwa daliban makarantar koyon jinya dake jami’ar College of Nursing Sciences dake Adazi-Nnukwu, jihar Anambra shawarar idan sun kammala karatunsu in suna son fita zuwa kasar waje yana goyon bayansu.

Peter Obi yace ya sha baiwa hukumar kula da malaman jinya ta Najeriya cewa su daina hana malaman jinya dake son fita kasar waje zuwa neman kudi da ingancin aiki.

Yace idan daliban suka ga cewa ba zasu samu abinda suke so ba a nan Najeriya ba laifi bane su tafi wani wajan dan samun abinda suke nema.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: Rarara Ya Bada Kyautar Naira Miliyan Goma Ga Waɗanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Maiduguri

Yace ba zasu baiwa daliban shawarar su zauna a inda abubuwa basa tafiya yanda ya kamata ba.

Yace duk wanda ke son ya fita zuwa kasar waje ba laifi bane yana iya fita ia tabbata idan suka gyara Najeriya daliban duk zasu dawo gida.

Ya bayar da misali cewa akwai babban hadiminsa, Michael-Jude wanda shima ya fita zuwa kasar waje, Peter Obi yace yanzu haka yana neman wanda zai masa aikin babban hadimi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *