Friday, August 14
Shadow

Shugaba Tinubu ya haramta sayo kayan da ake iyayi a cikin gida daga kasashen waje

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a kokarin karfafa tattalin arzikin Najeriya ya hana sayo kayan da ake iya yinsu a cikin gida daga kasashen waje.

Majalisar zartaswa tuni ta amince da wannan kudirin a zamanta na ranar Litinin inda aka bayyana cewa an yi hakanne dan karfafa masana’antun gida Najeriya.

Da yake magana ga manema labarai bayan zaman, ministan yada labarai, Mohammed Idris yace an dauki wannan mataki ne dan karfafa amfani da kayan da aka kerasu a cikin gida.

Yace sun kwaimwayi shugaban kasar Amurka, Donald Trump ne a kokarin da yake na karfafa masana’antun kasarsa ta Amirka

Karanta Wannan  Wata Sabuwa: Gwamnatin tarayya ta cire Tallafin CNG wanda a baya ta kawo tace shine zai maye man fetur ta fara bayar da tallafi a kanshi, Kuma har farashin ya tashi sosai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *