
Rahotanni sun bayyana cewa, na kusa da Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari sun yi kokarin ganin an tsayar da Sanata Ahmad Lawal takarar shugaban kasa a jam’iyyar ba Tinubu ba.
Rahoton yace wadannan mutane sun rubuta takardar Boge inda suka ce daga shugaban kasa ne suka mikawa shugaban ‘yansanda da shugaban DSS suka basu Umarnin su tabbatar Sanata Sanata Ahmad Lawal ne ya zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.
Saidai shugaban ‘yansandan a wancan lokacin ya nemi tabbatar da wannan umarni kai tsaye daga wajan shugaba Buhari inda Buharin yace ba gaskiya bane.
Hakan ya bayyana ne a sabon Littafin da aka rubuta da ya kunshi tarihin rayuwar tsohon shugaban kasar wanda aka kaddamar a fadar shugaban kasa jiya.