Friday, June 26
Shadow

Ji yanda na kusa da Buhari suka so a tsayar da Sanata Ahmad Lawal takarar shugaban kasa a APC

Rahotanni sun bayyana cewa, na kusa da Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari sun yi kokarin ganin an tsayar da Sanata Ahmad Lawal takarar shugaban kasa a jam’iyyar ba Tinubu ba.

Rahoton yace wadannan mutane sun rubuta takardar Boge inda suka ce daga shugaban kasa ne suka mikawa shugaban ‘yansanda da shugaban DSS suka basu Umarnin su tabbatar Sanata Sanata Ahmad Lawal ne ya zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.

Saidai shugaban ‘yansandan a wancan lokacin ya nemi tabbatar da wannan umarni kai tsaye daga wajan shugaba Buhari inda Buharin yace ba gaskiya bane.

Hakan ya bayyana ne a sabon Littafin da aka rubuta da ya kunshi tarihin rayuwar tsohon shugaban kasar wanda aka kaddamar a fadar shugaban kasa jiya.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Me magana da yawun Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana wata babbar Karama ta malamin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *