
Hukumomi a birnin Tokyo na kasar Japan sun kama wani mutum me suna Masato Watabe dan kimanin shekaru 79 bayan da ya hallaka mahaifiyarsa.
Mahaifiyar tasa nada shekaru 100 a Duniya kuma shine ke kula da ita.
Hukumomin birnin sun ce ya hallakata ne ya hanyar rufe mata baki.
Mutumin dai da kansa ya kirawo ‘yansanda.
Kasar Japan na fama da karancin matasa inda manyan mutane masu yawan shekaru dole sune ke kula da iyayensu da shakeru suka kamasu.