Ana zargin Wata matar aure me suna Omolara Oluwakemi ta kashe mijinta, Seidu Jamiu ta hanyar lafta mai tabarya akai yayin da yake bacci bisa zargin yana cin amanarta.
Lamarin ya farune a Akungba Akoko dake karamar hukumar Akoko North East dake jihar Onda a ranar 1 ga watan Yuni.
Sun shekara 7 da yin aure kuma suna da yara 3.
Wata majiya daga danginsu ta tabbatar da lamarin inda tace dama wannan rikici ya dade a tsakaninsu inda matar ke zargin mijin na cin amanarta.
Saidai kakakin ‘yansandan jihar, SP Funmilayo Odunlami-Omisanya ya tabbatar da faruwar lamarin saidai yace basu da tabbacin matar ce ta kashe mijin domin kuwa ita matar ce da kanta ta kai kara ofishinsu inda tace wani ya kashe mijinta.
Yace dan haka zuwa yanzu basu kama kowa ba, suna bincike ne tukuna.