
Rahotanni sun bayyana cewa, Jihar Lagos ta zo ta daya a Najeriya wajan yawan daliban da suka samu 5 credit a jarabawar NECO ciki hadda Turanci da Lissafi.
Dalibai 74,413 ne suka samu 5 credit a jarabawar NECO daga jihar Kano wanda hakan yasa Kano ta zo ta daya a Najeriya wajan yawan daliban da suka ci jarabawar.
Jihar dake biye mata itace jihar Lagos dake da dalibai 72,496 sannan sai jihar Oyo dake da yawan dalibai 55,543 da suka ci jarabawar.
Ko da a shekarar data gabata ma, Jihar Kano din dai itace ta zo ta daya wajan yawan daliban da suka ci jarabawar NECO.
Gwamnan jihar Kano ta bakin me magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana cewa, yana taya daliban, Malamsu da iyayensu murnar wannan nasara.