
Tsohuwar Tauraruwar fina-finan Hausa kuma Tsohuwar matar Sani Musa Danja, Mansurah Isah ta bayyana cewa tana rokon Tauraron kwallon Najeriya, Ahmed Musa ya bata kyauta Naira Miliyan 10.
Ta roki masoyan ta a kafafen sada zumunta dasu tayata rokon Ahmed Musa ya bata wannan kyauta.
Ta yi alkawarin cewa idan ya bata, zata baiwa mutane kyautar Naira Miliyan daya daga ciki.
