
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO tace kadaici na kashe mutane 871,000 duk shekara.
Rahoton yace a duk cikin mutane 6 na Duniya akwai mutum daya dake fama da kadaici wanda hakan ke haifar da cutuka kala-kala.
Masanan sun ce, kadaici na kara hadarin kamuwa da shanyewar rabin jiki, da ciwon zuciya, da ciwon sugar da damuwa da kisan kai.
Masana sun ce wayar hannu ta taimaka wajan saka mutane cikin kadaici inda ake samun karuwar masu kadaicewa da rashin son shiga mutane.