
Hukumar ‘yansandan a jihar Kogi tace ta iske gawar wani matashi me suna Sheriff Salifu da budurwarsa, Blessing tsirara a daki.
Lamarin ya farune a karamar hukumar Akpan ranar Juma’a April 18, 2025 inda ‘yansandan suka ce sun iske gawar masoyan tsirara a dakin matashin.
Kakakin ‘yansandan jihar, SP William Aya ya tabbatar da faruwar lamarin a sanarwar da ya fitar ga manema labarai a ranar Asabar.

Yace Blessing Adama dalibace a kwalejin ilimi ta jihar Kogi yayin da shi kuma Sheriff dan kasuwane.
Yace sun kai gawar masoyan Mutuware kuma sun fara bincike kan lamarin.