Monday, September 7
Shadow

Kai Duniya kalli Hotuna: Ji yanda aka iske gawar Sheriff Salifu da Budurwarsa, Blessing tsirara a dakinsa

Hukumar ‘yansandan a jihar Kogi tace ta iske gawar wani matashi me suna Sheriff Salifu da budurwarsa, Blessing tsirara a daki.

Lamarin ya farune a karamar hukumar Akpan ranar Juma’a April 18, 2025 inda ‘yansandan suka ce sun iske gawar masoyan tsirara a dakin matashin.

Kakakin ‘yansandan jihar, SP William Aya ya tabbatar da faruwar lamarin a sanarwar da ya fitar ga manema labarai a ranar Asabar.

Yace Blessing Adama dalibace a kwalejin ilimi ta jihar Kogi yayin da shi kuma Sheriff dan kasuwane.

Yace sun kai gawar masoyan Mutuware kuma sun fara bincike kan lamarin.

Karanta Wannan  Ganin Sheikh Dr. Ahmad Gumi a kasar Turkiyya ya jawo cece-kuce inda wasu ke cewa ya tsere ne saboda kharin da Amirka tace zhata Kawo Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *