
Tsohon hadimin shugaban kasa kuma shahararren dan jarida, Reuben Abati ya soki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu inda yace ya aikata laifin da ya kamata ace an tsigeshi.
Abati yace Gwamna ba zai ciru ba ta hanyar umarnin shugaban kasa ba.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi ranar Laraba a gidan talabijin na Arise TV.
Hakan na zuwane bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dakatar da gwamnan jihar Rivers Simi Fubara daga mukaminsa.
Reuben Abati ya bayyana cewa, shugaba Tinubu ta take doka wajan daukar wannan mataki na dakatar da gwamnan jihar ta Rivers.
Abati yace wannan mataki da Tinubu ya dauka ya sashi ya zama me mulkin kama karya dan yanzu ya zama me yiwa majalisar jihar Rivers doka hakanan duk dokar da za’a yi amfani da ita a jihar Rivers daga sama ne za’a aikata.
Yace kuma wannan abubuwa da yayi sun isa su sa a tsigeshi daga kan mukaminsa na shugaban kasa.