Abinda me kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg yayi a wajan rantsar da shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya dauki hankula.
Bidiyo ya nuna Mark Zuckerberg yana kallon nonuwan matar me kamfanin Amazon, watau Jeff Bezos. Lamarin ya jawo cece-kuce sosai inda wasu ke ganin itama bai kamata ta yi irin wannan shigar ta nuna kirji ba a wajan taro me muhimmanci irin wannan ba.
Manyan masu kudin Duniya da suka mallaki kamfanonin sadarwa dana kasuwanci irin su Facebook, Amazon, Tiktok, Apple da saransu duk sun halarci wajan taron rantsar da Donald Trump.