
Kalaman Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani na cewa El-Rufai ba me gidansa ne a siyasnce ba sun jawo cece-kuce.
Gwamna Uba Sani ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a Channels TV inda yace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da Lauya Gani Fawehinmi ne iyayen gidansa a Siyasa.
Saidai hakan yasa wasu komawa baya a tarihi inda suka zakulo wata tsohuwar magana da Gwamnan ya taba yi inda yace El-Rufai me gidansa ne a siyasa.