
Tauraron Mawakin Siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa, ba karamin kusanci gareshi da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba.
Rarara yace bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya zama shugaban kasa sau 11 yana zuwa yana ganin shugaban kasar.
Yace bai taba zuwa zai ga shugaban kasa ba aka hanashi.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a kafar DCLHausa.
Rarara yace shi mawakin shugaban kasa ne wanda kuma shugaban kasar ya yadda shi mawakinsa ne.