
Wani me suna Murtala Gamji, Shugaban dattawan Matasan Najeriya ya bayyana cewa ba zasu bari a rika taba malamai suna kyalewa ba.
Ya bayyana hakane a wata bidiyo da kafar ATP Hausa ta wallafa.
Ya kara da cewa, ko da fasto na garine aka ci zarafinsa ba zasu bari ya wulakanta ba zasu fito su kareshi.
Da yake jawabi da kuma ikirarin baiwa Sheikh Bala Lau Kariya, ya kara da cewa, Dan Bello bashi da asali me kyau.
Inda yace asalin mahaifinsa sata ya je yi a makabarta aka bishi, tun daga nan ne ya bar garinsu na Galadanci har yau bai dawo ba.
Kalli Bidiyon a kasa:
Me zaku ce?