
Babban Malamin Addinin Islama, Farfesa, Mansoor Sokoto ya bayyana cewa, basu ji dadin Nasarar da Iran ta samu ba.
Ya bayyana hakane a wajan wata hudu ba da yayi inda aka ji yana cewa Iran ta samu nasarar karkatar da zukatan Musulmai su sota.
Malam ya bayyana cewa An samu wasu malamai da suka rika jawo ayoyin kur’ani da Hadisai suna nuna goyon baya ga Iran.
Ya kuma zargi Iran da shirka da bautar wanin Allah.
A kwanannan ne dai aka gwabza fada tsakanin kasar Iran da Israyla wanda har kasar Amurka ta shiga fadan.