
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, bai taba neman tikitin tsayawa takarar shugaban kasa yayi rashin nasara ba.
Ya bayyanna hakane yayin da ‘yan jarida ke tambayarsa shin ko yana ganin zai iya samun tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar ADC?
Atiku da kuma aka tambayeshi kan ba zai hakura ya barwa matasa ba? Yace ai Dimokradiyya ake yi, matasan su fito au nema.
Atiku da wasu ‘yan Adawa da yawa ne dai suka hada kai suka koma jam’iyyar ADC.