Hukumar kula da ababen hawa ta jihar Legas, LASTMA ta tabbatar da mutuwar mutane 3 bayan da motar Dangote ta bugesu.
Rahoton Daily Post yace motar Dangoten dake tafiya akan titin Ita-Opo, Epe ta samu matsalar birki ne inda hakan yasa ta yi taho mu gama da wasu motocin.
Shugaban hukumar ta LASTMA, Olalekan Bakare-Oki ya tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakin hukumar Taofiq Adebayo, yace motar ta Dangote ta buge Keke Napep da wata mota dake ajiye a gefe.
Yace direban keke Napep din da dalibai biyu daga makarantar Manpower Technical School sun mutu sanadiyyar hadarin