Monday, December 9
Shadow

Kalli Bidiyo da hotuna yanda motar Dangote ta buge mutane 3 suka mùtù a Jihar Legas

Hukumar kula da ababen hawa ta jihar Legas, LASTMA ta tabbatar da mutuwar mutane 3 bayan da motar Dangote ta bugesu.

Rahoton Daily Post yace motar Dangoten dake tafiya akan titin Ita-Opo, Epe ta samu matsalar birki ne inda hakan yasa ta yi taho mu gama da wasu motocin.

Shugaban hukumar ta LASTMA, Olalekan Bakare-Oki ya tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakin hukumar Taofiq Adebayo, yace motar ta Dangote ta buge Keke Napep da wata mota dake ajiye a gefe.

Karanta Wannan  Jikan Shehu Ibrahim Inyass Ya Bada Tallafin Ragunan Layya Guda 462 Ga Mabukata

Yace direban keke Napep din da dalibai biyu daga makarantar Manpower Technical School sun mutu sanadiyyar hadarin

Karanta Wannan  Hotuna: Wannan bawan Allahn ya tsero daga hannun 'yan Bìnďìgà a jihar Zamfara bayan kwanaki 47 suna rike dashi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *