Friday, December 5
Shadow

Kalli Bidiyo: Dama me ya hada dan Izala da yin fim? Ai Maulidi ne asalin fim, daga nan ake samun ci gaba a fara harkar Fim>> Sheikh Lawal Triumph ya mayarwa da Tauraron fina-finan Hausa, Tijjani Faraga martani bayan da yace shi ba dan Izala bane

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Malamin addinin Islama, Sheikh Lawal Triumph ya bayyana cewa dama babu abinda ya hada dan Izala da yin fim.

Ya bayyana hakane a matsayin martani ga kalaman tauraron fina-finan Hausa, Tijjani Faraga bayan da yace shi ba dan izala bane kuma duk wanda ya kara hadashi da Izala bai yafe ba.

Lawal Triumph yace dama daga Maulidi ake fara harkar fim idan an samu ci gaba shine za’a shiga a ci gaba a kai masana’antar fina-finan Hausa.

Malam yace Tijjani yana tunanin ya zagi Izala ne amma yabonta yayi, yace dan babu dan fim dan izala, babu boka dan izala, babu dan daudu dan Izala.

Karanta Wannan  INNA LILLIHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN: Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida Dake Lapai A Jihar Neja Ta Yi Rashin Dalibai Biyu A Rana Daya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *