
Shahararren dan fim din Hausa, Rabiu Rikadawa wanda aka fi sani da Baba Dan Audu ya bayyana cewa yana rokon masu cewa ya mutu su daina.
Ya bayyana hakane a wani Bidiyo da ya saka a shafinsa na sada zumunta.
Yace mutane na ta kiransa da cewa wai an ce ya mutu.
Yace dan Allah a bari mutuwar gaskiyar ta zo.
Ya baiwa mutane musamman masoyansa hakuri.