
Babban Malamin addinin Islama Sheikh Aminu Daurawa ya mayar da martani kan labarin da Dan Bello yayi na cewa, an baiwa Shugaban kungiyar Izala, Sheikh Bala Lau Kwangilar gina azujuwa amma ba’a yi su ba.
A bidiyon da hutudole ya ci karo dashi yana yawo a kafafen sada zumunta, Mun ji malam na cewa shi fa me da’awa ba ma’asumi bane.
Yace yau idan aka ce ga malami yaci kudin wani dan kada a zubar masa da mutunci kamata yayi mutane su hada kudi su biya.
Yace akwai wani abu da yaje nema wani ofis amma ya bashi wahala inda wani yace malam ya daina wahalar da kansa yace akwai karuwar me ofis din da zaiwa magana a bashi abinda yake nema.
Yacw karuwai ana basu kwangilar Biliyan da ‘yan Daudu amma malamai basa samun wannan dama.