
Malamin Addinin Islama, Farfesa Sheikh Isa Ali Pantami ya bukaci mutane su daina barin mata a gida suna musu girki kawai.
Malam yace mata ma suna da irin fikirar da Allah ya hore musu wadda za’a iya amfani da ita wajan ci gaban Al’umma.
Dan haka yace kada a ajiye mace girki kawai ta sani, a rika basu dama suna sana’a dan samun taro sisi.
Malam yace akwai inda mata suke yin abinda maza basu iya yi hakanan akwai inda maza ke yin abinda mata basu iya yi.