
Wani matashi daga jihar Katsina wanda yace ya fito ne daga garin Radda na jihar katsina kuma da uwane a wajan gwamnan Katsina watau Dikko Raddah ya koma Kirista.
Matashin wanda yace sunansa Abdullahi yace ya koma Kirista ne a Makaranta bayan da ya fara karanta Baibul ya kuma fahimceshi.
Matashin yace da ya gayawa mahaifiyarsa ta dauki abin da wasa amma daga baya da aka ga da gaske yake, an kamashi an daure tsawon watanni indaa yace amma duk da haka bai koma musulmi ba.