
Tauraron mawakin Hausa Naziru Sarkin Wakar Sarkin Kano ya bayyana cewa sabuwar motarsa ta G-Wagon Mercedes Benz zata sayi motar Dauda Kahutu Rarara 3 hadda canji.
Ya bayyana hakane a wani Bidiyon da ya wallafa da ya yadu sosai a kafafen sada zumunta.
Sarkin Waka yace ya sayi motar ne dan hucewa wani masoyinsa Haushi saboda gorin motar da aka masa.
Nazir yace kuma da ake cewa wai an wuceshi, ko hangoshi ba’a yi ba.
Duk da cewa, Sarkin Waka bai kira suna ba amma da yawa sun yi Amannar cewa da Dauda Rarara yake.