Kamfanin matatar man fetur ta Dangote ta wallafa Bidiyon da ya nuna motocin jigilar Man fetur da suka fara jigilar man a matatar man fetur din.
An fara jigilar man fetur dinne daga matatar man fetur ta Dangote bayan Dambarwar da aka sha ta cece-kuce tsakaninsa da Kamfanin mai na kasa NNPCL da kuma Gwamnatin Tarayya.