Wata ma’aikaciyar Jinya,Nurse dake aiki a wani Asibiti dake Bihar me suna RBS Health Care Centre ta gamu da barazanar fyade.
Likitan Asibitin da take aiki da wasu 3 ne suka so yi mata fyade amma basu yi nasara ba.
Likitan me suna Dr Sanjay Kumar da abokan aikinsa, Sunil Kumar Gupta da Awadhesh Kumar ne suka aha giya suka yi mankas.
Suka kulle kofofin shiga Asibitin inda suka afka mata. Nan dai Allah ya bata sa’a ta kama azzakarin babban likitan ta yanke da wukar fida.
Ta samu ta fita da gudu kamar yanda kafar Livemint ta ruwaito. Ta samu wani waje ta labe inda ta kira ‘Yansanda suka zo suka kama likitocin.
Likitan dai yana can yana karbar kulawa ta musamman inda ake ci gaba da bincike.