
A jiya ne dai shahararren mawakin siyasa na tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, watau Dauda Kahutu Rarara ya wallafa sakon ta’aziyyar tsohon shugaban kasar a shafinsa na sada zumunta.
Rarara ya wallafa Bidiyon wakar ta’aziyyar da yawa Marigayi tsohon shugaban kasar.
Saidai da yawan masoya Buharin sun sokeshi da rashin wallafa sakon tun da aka yi rasuwar.
Wasu sun ce sai da ya ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a wajan jana’izar sannan ya yi ta’aziyyar.
A gefe guda kuma wasu na kiransa da butulu.
Hakanan Rarara ya sha caccaka inda wasu ke cewa ba da waka ya kamata ace yayi ta’aziyyar ba.
Dangantaka ta yi tsami tsakanin Rarara da Buhari bayan saukar Buharin daga mulki inda a lokuta daban-daban aka rika jin Rarara din na sukar Buhari.



www.facebook.com/share/v/16RijPXM4q/