‘
Yan Bindigar da suka yi garkuwa da tsohon janar din soja kuma tsohon shugaban hukumar bautar kasa(NYSC) Janar Maharazu Tsiga rtd sun nemi a biya Naira Miliyan 250M a matsayin kudin fansarsa.

Wata majiya dake kusa da iyalan janar dinne suka bayyana hakan inda suka ce masu garkuwa da mutanen sun kira iyalan janar din suka sanar da hakan.
An yi garkuwa da janar tsiga ne tare da wasu mutane 9.
Lamarin ya faru ranar Laraba da dare inda ‘yan Bindiga su kusan 100 suka zagaye gidansa suka tsafi dashi.
Dan majalisar tarayya dake wakiltar Bakori da Danja ya tabbatar da faruwar lamarin saidai zuwa yanzu hukumomin soji dana ‘yansanda basu bayar da ba’a si ba kan lamarin.