
Tawagar Gwamnatin tarayya data hada da Ministoci 25 da gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum wadda mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya jagoranta ta sake komawa gidan Marigayi, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari inda sukawa iyalansa ta’aziyya.
A jiya ne dai aka yi jana’izar Buhari a gidanda dake Daura wadda ta samu halartar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu