
A ranar Juma’ar data gabata ne aka daura auren dan Sanata Abdulaziz Yari a Masallacin Sultan Bello Kaduna.
Shugaban Izala,Sheikh Bala Lau ne ya ya gabatar da huduba kamin zuwan liman.
Saidai a yayin da yake wa’azi, Alaramma Ahmad Sulaiman na ja masa baki, sai ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya shiga masallacin.
Ai kuwa nan da nan Sheikh Bala lau ya janye lasifika daga bakin alaramma Ahmad Sulaiman yana tsaka da karatun Qur’anin ya tafi gaisawa da shugaba Tinubu.
Hakan ya jawo cece-kuce sosai inda wasu ke ganin bai kamata ba.