Tuesday, April 28
Shadow

Kalli Bidiyo: Yanda Shugaban Izala Sheikh Bala Lau ya janye Lasifika daga bakin Alaramma Ahmad Sulaiman yana tsaka da karanta Qur’ani ya tafi gaisawa da shugaba Tinubu ya jawo cece-kuce

A ranar Juma’ar data gabata ne aka daura auren dan Sanata Abdulaziz Yari a Masallacin Sultan Bello Kaduna.

Shugaban Izala,Sheikh Bala Lau ne ya ya gabatar da huduba kamin zuwan liman.

Saidai a yayin da yake wa’azi, Alaramma Ahmad Sulaiman na ja masa baki, sai ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya shiga masallacin.

Ai kuwa nan da nan Sheikh Bala lau ya janye lasifika daga bakin alaramma Ahmad Sulaiman yana tsaka da karatun Qur’anin ya tafi gaisawa da shugaba Tinubu.

Hakan ya jawo cece-kuce sosai inda wasu ke ganin bai kamata ba.

https://www.tiktok.com/@muhammadsunnahaljosawy/video/7552481590450900231?_t=ZS-8zvFbjBS0LA&_r=1
Karanta Wannan  Ba gaskiya bane, Ban sha komai ba, Matukin jirgin saman Air Peace ya karyata binciken da yace ya sha miyagun Qayoyi da Giyya a lokacin da yake tuka mutane 103

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *