
Rahotanni daga Falasdinu na cewa, Sojojin kasar Israela, IDF sun budewa taron Falasdiynawa wuta a yayin da suka taru suke karbar tallafin abinci.
Lamarin yayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla mutane 22.
Wakilin majalisar Dinkin Duniya ya bayyanawa Kamfanin dillancin labaran AFP cewa raba kayan tallafi a gaza ya zama tarkon Mutuwa.
Kungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta tabbatar da faruwar lamarin.
Saidai wata gidauniyar agaji a Gaza tace rahoton bashi da inganci.