Sunday, November 16
Shadow

Ma’aikatan Shari’a zasu tsunduma yajin aikin sai mama ta gani gobe, Litinin

Rahotanni sun bayyana cewa, Ma’aikatan shari’a na Najeriya karkashin Kungiyarsu ta (JUSUN) sun nace akan tafiya yajin aiki gobe, Litinin, 2 ga watan Mayu.

Ma’aikatan bangaren babbar kotun tarayya ne zasu tafi yajin aikin inda bangaren kotun Koli suka fasa shiga yajinnaikin.

Wata majiya tace shugaban hukumar DSS ya zauna da ma’aikatan tsawon awanni 4 amma duk da haka sun ce ba zasu fasa tafiya wannan yajin aikin ba.

Sakataren kungiyar, Comrade Mohammed Isah yace zasu fara yajin aikin gobe Litinin inda yace yana kiran duka ma’aikatansu da su zauna a gida kada su je wajan aiki.

Saidai yace a goben ma akwai wani zama sa za’a sake yi.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Hadiza Gabon baki kyauta kin ba, Na yi Hira dake kin je kin yi Editing ana ta Zhagina>>Inji Tauraron fina-finan Hausa, Musbahu Anfara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *