Wani Bidiyon wata budurwa ya bayyana a kafafen sada zumunta inda aka ganta ta ruga da gudu zata rungumi gwamnan jihar Kano,Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida.
Tuni dai jami’an tsaron dake tare da gwamnan suka tare matar kamin ta karasa kan gwamnan.
Da yawa sun bayyana mamaki da ganin hakan inda aka rika cewa rungumarsa ta so ta yi.