Wednesday, December 11
Shadow

Matsalolin Nijeriya Na Bukatar A Yi Musu Taron-Dangi Domin Ganin An Yaki Talaùcin Da Ya Addabi Al’ummar Kasar, Inji Kashim Shettima

Matsalolin Nijeriya Na Bukatar A Yi Musu Taron-Dangi Domin Ganin An Yaki Talaùcin Da Ya Addabi Al’ummar Kasar, Inji Kashim Shettima

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya kara jaddada bukatar hada karfi da karfe tsakanin gwamnati, da abokan huldarta, da sauran masu ruwa da tsaki don kawar da talauci da inganta rayuwa ga daukacin ‘yan Nijeriya.

Shettima, ya fadi hakan ne a wajen taron majalisar tattalin arzikin kasa karo na 144 a Abuja, inda ya jaddada cewa, samar da yanayin da kowane dan Najeriya ke da damar ci gaba, abu ne da ke bukatar hadin kai.

Sanatan ya yaba da gudunmawar da masu ruwa da tsaki da suka hada da gidauniyar Bill & Melinda Gates da kuma rukunin kamfanonin Dangote suke bayarwa wajen gina ci gaban Najeriya a fannonin da suka shafi lafiya, abinci mai gina jiki, noma, da ilimi.

Karanta Wannan  WATA SIYASAR SAI KANO: Shi Ma Sanata Barau Jibrin Zai Aurar Da 'Yarsa A Fadar Sarki Aminu Ado Bayero, Kamar Yadda Kwankwaso Ya Aurar Da 'Yarsa A Fadar Sarki Sanusi II

Taron na NEC ya kuma tattauna kan dabarun da za a bi don magance matsalar ambaliyar ruwa, da rashin abinci mai gina jiki, sannan da yadda za a samar da ‘yan sandan jihohi, da maganin cutar shan inna, ciki kuwa har da bukatar a aiwatar da shawarwarin da aka amince da su a kwamitin wucin-gadi kan ambaliyar ruwa, zaizayar kasa, fari da kwararowar Hamada, kana da kafa kwamitin kula da harkokin kiwon lafiya, da kuma kawar da Cutar Polio).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *