
Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yansanda sun kama Jarumin Tiktok, Hassan Make-Up.
A wani Bidiyo da aka ganshi a ofishin ‘yansanda, An ga Dansandan dake masa tambayoyi ya mareshi tare da zagi wanda hakan ya sabawa dokar aikin dansanda.
Ko da a jiya, saida Kwamishinan ‘yansanda na birnin tarayya, Abuja ya ja kunnen jami’ansa cewa, zagi da marin wanda ake zargi ko me laifi baya cikin aikin dansanda.
Rahoton da muke samu shine Hassan Make-Up ya zo bikin Rarara ne aka kamashi.