
Tsohon Minista, Sanata Adeseye Ogunlewe ya bayyana cewa, Kyawun da Sanata Natasha Akpoti ke dashi shine babbar matsala a gareta.
Ya bayyana hakane a yayin da ake hira dashi a gidan talabijin na Arise TV.
Yace kyan da sanata Natasha Akpoti ke dashi, babu yanda za’a yi namiji me lafiya ya ganta ya kyale.
Yace kuma su mata sanatoci suma suna magana da izza ta yanda baka isa kace musu mata ba, idan ka sake ma ka ce musu su mata ne zasu iya ganin kamar kana son ka rainasu ro za’a iya samun matsala.
Yace Mace kamar Sanata Natasha Akpoti idan ta wuce dole ka bi da kallo, kadan kanne ido ko ka daga mata gira, ko da kuwa ace baka mata magana ba.
Yace kuma hakan ba matsala bane dan dabi’a ce ta namiji, yace babu yadda za’ayi sanata Natasha Akpoti ta wuce kace zaka rufe ido baka kalleta ba.