Monday, December 16
Shadow

Kalli Bidiyo: Yara ‘yan shekaru 15 zuwa 16 su 3 uwarsu daya ubansu daya wanda aka dauka daga Najeriya aka kaisu suna ka-ru-wan-ci a kasar Ghana

Bidiyon wasu kananan yara ‘yan mata dake tsakanin shekaru 15 zuwa 16 su 10 da aka dauka daga Najeriya aka kaisu kasar Ghana yin karuwanci ya tayar da hankula.

Bidiyon ya watsu sosai a shafukan sada zumunta inda aka gansu ana tambayarsu kowace na fadin shekarunta da jihar data fito, yawancinsu sun fito ne daga jihar Imo kuma daga cikinsu akwai guda 3 wanda uwarsu daya ubansu daya.

Ko da aka tambayesu iyayensu sun san sun tafi karuwanci? Sai suka ce a’a.

Lamarin dai ya dagawa mutane hankula sosai inda akai ta musu Allah wadai.

Karanta Wannan  Gwamnatin Abba a Kano ta biya kudin hayar gida ga diyar Marigayi Ado Bayero

Tuni dai gwamnatin tarayya ta sanar da fara bincike kan lamarin.

Ama kan hakane Gwamnatin ta yi sabuwar dokar da ta hana zuwan kananan ‘yan mata da basu cika shekaru 18 ba zuwa Otal.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *