
Attajirin Africa, Aliko Dangote a hukumance ya sanar da mayar da matatar man fetur dinsa ta rika fitar da ganga Miliyan 1.4 kullun Maimakon Ganga 650,000 da yake fitarawa a yanzu.
Yace hakan zai sa matatar tasa ta zama ta Daya a Duniya wajan yawan fitar da man fetur.
Dangi ya sanar da hakane a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai.
Ya godewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da kuma ‘yan Najeriya bisa hadin gwiwar da suka bashi.