
Bidiyon abin kunyar da ya faru a jihar Ogun na ta yawo a kafafen sadarwa inda aka ga ‘yan Najeriya na rokon ‘yan kwallon kafar kasar Africa ta Kudu abinci.
‘Yan kwallon wanda suka je filin kwallo na MKO Abiola dake Abeokuta dan wasa da Remo Stars sun rika jefawa ‘yan Najeriyar sauran abincin da suka ci suka rage.
Da yawa dai sun yi Allah wadai da mutanen.