
Wani dan kasar Morocco ya tsaya a kusa da motar ‘yan kwallon Najeriya, Super Eagles inda ya rika nuna kasarsu zata yi nasara akan Najeriya.
Ya daga kyamararsa inda ya dakko Bidiyon Osimhen dake zaune a cikin motar, Osimhen ya daga masa hannu.
Lamarin ya dauki hankula a kafafen sada zumunta.
