
Ana ta kiraye-kirayen jami’an tsaro su kama wannan malamin saboda kalaman da yayi Biyo bayan rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Da yawan masu kiran sun ce irin kalaman da yake yi na kamanceceniya da na masu tsaurin ra’ayin addini irin su kungiyar Bòkò Hàràm da ÌŚWÀP.
Daya daga cikin masu kiran a yi bincike akan malamin shine Zagazola Makama wanda yace duk da ba’a samu wata alaqa tsakanin malamin da wata kungiyar ta’addanci ba amma ya kamata a bicikeshi.