Monday, December 15
Shadow

Kalli Bidiyon: Bataliyar sojoji guda ce ke bin Dan shugaban kasa, Seyi Tinubu suna bashi kariya, Sam hakan bai dace ba>>Inji Farfesa Wole Soyinka

Farfesa Wole Soyinka ya yi suka ga yanda ake baiwa dan shugaban kasa, Seyi Tinubu tsaro da sojoji masu yawa.

Yace yawan sojojin dake baiwa dan shugaban kasar tsaro sun isa su dakile yunkurin juyin mulki a kasar Benin Republic, yace da Shugaba Tinubu kawai Seyi ya kira yace ya je da sojojin da suke bashi kariya su hana juyin mulki a kasar Benin Republic ba sai ya tura sojoji ba.

Yace ya taba zuwa otal ya hadu da dan shugaban kasar yaga sojojin da suke bashi kariya inda yace sun yi yawa.

Yace dan shugaban kasa bai kamata ana bashi irin wannan sojoji ba.

Karanta Wannan  Fada ya kare tsakanin mu, mun shirya>>Wike da Fubara bayan da Shugaba Tinubu ya sasantasu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *