
Me baiwa gwamnan Kano shawara akan harkar siyasa, Sanusi Sirajo Kwankwaso ya bayyana cewa, ya ajiye aikinsa.
Ya bayyana cewa ya ajiye ne dalilin fitar da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi daga jam’iyyar NNPP yana shirin komawa APC.
Yace shi ba zai ci amana ba kuma ba zai bi Butulu ba.
Yace ya kai takardar ajiye aikin an ki karba shine yace bari ya fito kafar sada zumunta ya sanar da ajiye aikin nasa.